Roma
Milan
An kayatar da titunan Italiya da Hotunan shahid Qassim Sulemani Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA24-an lika hotunan Janar Qassim Sulemani a manyan biranen Italiya kamar Roma da Milan, wata kungiya mai suna ‘yan gwagwarmar Turai don ‘yanta Siriya ne suka dauki nauyin lika Hotunan. ‘yan wannan kungiya suna girmama shahid Sulemani a matsayin wani gwarzo kuma abun koyi. Wannan lika Hotunan ya zo dai dai da cika kwanaki 40 da shahadar Qassim Sulemani tare da abu Mahdi almuhandis.